9 Afirilu 2026 - 15:48
Source: ABNA24
Hizbullah Na Ci Gaba Da Ruwan Makamai Akan Garuruwan Isra'ila 

A Sanarwa ta 7 na gwagwarmayar Musulunci ta Lebanon ta kai hari kan taron sojan Isra'ila a Al-Marj.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hizbullah ta sanar a cikin wata sanarwa: don kare Lebanon da al'ummarta da kuma mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da makiya ke yi, mayakan gwagwarmayar Musulunci da karfe 11:30 na safe a ranar Alhamis, 9 ga Afrilu, 2026, ta kai hari kan gungun sojojin Isra'ila "Al-Marj" da makami mai linzami. 

Sannan Hizbullah tayi ruwan makamai masu linzami a garin "Kriat Shamuneh" a karo na shida tun da safiyar yau. Kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa, mayakan gwagwarmayar sun harba rokoki a karo na shida da karfe 13:30 na kasar. 

Za a ci gaba da wannan martani har sai Isra'ila-Amurka sun dena kai hari a kan kasarmu da al'ummarmu. 

Your Comment

You are replying to: .
captcha